Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai iol.co.za ya bayar da rahoton cewa, musulmi a yankin Sydenham da ke cikin gundumar Durban a kasar Afrika ta kudu sun nuna takaici kan matakin da wata makaranta da ke yankin ta dauka, na hana dalibai mata musulmi saka lullubi.
A cikin wani bayani da cibiyoyin musulmi na yankin da ma wasu yankuna na kasar Afrika ta kudu suka fitar kan batun sun, kirayi mahukunta a bangaren ilimi da su sanya baki a cikin lamarin.
Faisal Sulamin daya daga cikin jagororin musulmi a kasar Afrika ta kudu, ya bayyana mataki da cewa ya yi hannun riga da abin da ke cikin kundin tsarin mulkin kasar, wanda ya bukaci da a baiwa kowane dan kasa damar yin addininsa daidai da koyarwar addinin nasa.
Ya ce saka hijabi ga mata umarni ne na addinin musulunci, a kan ya ce suna kira da babbar murka ga mahukunta da su dauki dukkanin matakan da suka dace domin kare ma musulmi hakkokinsu a fadin kasar ta Afrika ta kudu.