IQNA

Saudiyya Ta Rusa Masallatai 1024 A Yemen

23:03 - May 18, 2019
Lambar Labari: 3483650
Bangaren kasa da kasa, kusa a kungiyar Ansaullah ya ce daga lokacin da Saudiyya ta fara kaddamar da hare-hare kan kasar Yemen shekaru zuwa yanzu ta rusa masallatai 1024 a fadin kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, Adanan Kuflah kusa a kungiyar Ansaullah ya ce daga lokacin da Saudiyya ta fara kaddamar da hare-hare kan kasar Yemen shekaru zuwa yanzu ta rusa masallatai 1024 a fadin kasar baki daya, wadanda wasu daga cikin wadannan masallatai ko dai sahabban manzon Allah suka gina su, kuma Ahlul bait (AS).

Ya ci gaba da cewa, babu wani abu da yake da matsayi a tarihin addinin musulunci da kea kasar Yemen wanda Sauiyya ta bari.

Baya ga masallatai akwai wurare masu tsohon tarihi na dubban shekaru tun kafin addinin musulunci, wanda ko bayan zuwa musulunci an ci gaba da kiyaye su, domin manzon Allah bai bayar daumarnin a rusa su ba, kamar yadda kuma sahabbai ba su yi hakan, amma gwamnatin Saudiyya ta rusa su.

Baya ga irin wadannan wurare masu muhimmancia  tarihin musulunci dama tarihi na dan adam, masarautar al saud ta rusa asibitoci, da kasuwanni, cibiyoyin ilimi da marantu, da madatsun ruwa gami da tashoshin wutar lantarki, kuma haka duk yana faruwa ne a kan idanun al'ummomin duniya har da majalisar dinkin duniya.

3812578

 

captcha