IQNA

‘Yan Adawa A Sudan Sun Nuna Damuwa Kan Dakatar Da Tattauwar Da Sojoji Suka Yi

23:54 - May 16, 2019
Lambar Labari: 3483646
Jam’iyyun siyasa a Sudan, sun nuna takaici kan matakin da majalisar sojin kasar ta dauka na dakatar da tattaunawa a tsakaninsu.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, a ikin wani bayani da suka fitar a daren jiya, jim kadan bayan sanarwar da sojoji suka bayar kan dakatar da tattaunawar da ake tsakanin bangaren majalisar soja da kuma sauran bangarorin siyasa, Jam’iyyun siyasa masu adawa da kuma kungiyoyin farar hula masu fafutuka, sun yi kakkausar suka kan majalisar sojin.

Gamayyar jam’iyyun adawa  akasar ta Sudan ta bayyana cewa, wannan mataki na majalisar sojin Sudan, yunkuri ne na neman wanzar da ci gaban kama karya  akasar, a daidai lokacin da al’umma suke bukatar mulki na dimukradiyya, wanda zai kare manufofinsu da ‘yancinsu an siyasa.

Kafin haka dai sojojin sun sanar da cewa sun cimma matsaya tare da bangarorin siyasar kasar, dangane da kafa gwamnatin rikon kwarya wadda za ta hada dukkanin bangarori, kuma za ta jagoranci kasr har tsawon shekaru kafin gudanar da zabe.

3812101

 

 

 

 

captcha