IQNA

An tarjama Kur’ani A Cikin harshen Ebira A Najeriya

22:56 - May 05, 2019
Lambar Labari: 3483609
Bangaren kasa da kasa, an tarjama kur’ani mai tsarkia  cikin harshen Ebira a jahar Kogi da ke Najeriya.

Bangaren kasa da kasa, an tarjama kur’ani mai tsarkia  cikin harshen Ebira a jahar Kogi da ke Najeriya.Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na tawasul ya habarta cewa, an kaddamar tarjamar kur’ani mai tsarki a  cikin harshen Ebira a jahar Kogi da ke Najeriya.

Abdulmumin Ahmad Aukar wakilin gwamnatin jahar, da kuma Adnan Butaji jakada Saudiyya a Najeriya, sun gabatar da jawabi.

Jakadan Saudiyya a Najeriya ya cewa, bababr cibiyar buga kur'ana ta Madina, ya zuwa shekara ta 2019 ta buga kur'anai miliyan 311, da dubu 882 da 269, wanda aka raba su ga kasashe da suka hada da a Afrika, kamar yadda aka tarjama kur'ania  cikin harsuna 70, kuma 18 na Afrika.

Adnan Bustaji ya e an ware kwafi 500 domina jiye su a masallacin babban birnin Jiha.

Najeriya dai ita e kasa mafi girma  a nahiyar Afrika, inda a halin yanzu take da mutane miliyan dari biyu, kuma an tarjama kur'ani da harsuna daban-daban na kasar da suka da Ebira a halin yanzu.

3808932

 

 

captcha