IQNA

Kasashen Afrika 30 Za Su halarci gasar Kur’ani ta Duniya A Masar

22:38 - March 10, 2019
Lambar Labari: 3483441
Bangaren kasa da kasa, kasashen Afrika 30 ne daga cikin kasashe 50 da za su halarci gasar kur’ani mai tsarki ta duniya a kasar Masar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ministan ma’ikatar kula da harkokin addini a Masar Mukhtar Ali juma’a ya bayyana cewa, kasashen Afrika 30 ne daga cikin kasashe 50 da za su halarci gasar kur’ani mai tsarki ta duniya a kasar Masar ya zuwa yanzu haka.

Wanann gasar Kur’ani dai za a gudanar da ita ne a yankin Jizah daya daga cikin yankuna da ake mayar da hankali matuka ga hardar kur’ani mai tsarkia  kasar ta Masar.

Bayanin ya ci gaba da cewa yanzu haka baki sun fara hallara domin fara shirye-shiryen gasar, wadda za ta kasance irinta ta farko da za a gudanar a wanann yanki.

Cibiyar kula da harkokin kur’ani ta kasar masar karkashin ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar ce za ta dauki nauyin shirya gasar.

Mahardata da makaranta satin ne za su kara da juna  awannan gasa, inda za a gudanar da gasar a bangarori na harda da tilawa da kuma hukunce-hukuncen karatun kur’ani mai tsarki.

3796584  

 

 

captcha