Kamfanin dillancin labaran iqna, Adnan Husaini ministan Palestine mai kula da harkokin Quds ya bayyana cewa Isra’ila na rarraba masallacin Aqsa zuwa bangarori daban-daban.
Ministan ya ce irin matakan da Isra’ila take dauka a halin yanzu a kan masallacin qasa na nuni da irin shirin da take da shi ne na rarraba wannan masallaci.
Ya ce masallacin Aqsa wakkafi na musulmi da babu yadda za a yi a raba shi, kuma daukar duk wani mataki makamancin wannan ba a bu ne da dukkanin musulmi na duniya za su amince da shi ba.
A jiya ne sojojin Isra’ila suka kaddamar da farmaki a kan masallacin Aqsa tare da rufe kofar babau rahma, wadda it ace kofar da muuslmi suke shiga cikin masallaci, inda suka jikkata musulmi da dama tare da kame wasu.