IQNA

Manzon Musamman Na MDD A Yamen Ya Gana Da Jagoran Ansarullah

22:49 - February 18, 2019
Lambar Labari: 3483382
Manzon musamman na majalisar dinkin duniya kan rikicin Yemen Martin Griffiths ya gana da shugaban kungiyar Ansarullah Abdulmalik Badruddin Alhuthi a birnin San'a.

A yayin ganawar tasu, bangarori biyu sun tattaunawa kan muhimman lamurra da suke cima al'ummar kasar ta Yemen tuwo a kwarya, da kuma batun yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma a Sweden, wadda har yanzu kawancen da Saudiyya ke jagoranta wajen kaddamar da yaki kan al'ummar kasar ta Yemen bai yi aiki da ita ba.

Baya ga haka kuma tattaunawa ta tabo isar da taimakon gaggawa ga bangarorin al'ummar kasar da suke bukatar taimako, musamman na magunguna da abinci da kuma kayan bukatun rayuwa wadanda suka gagare su sakamakon yakin da Saudiyya take kaddamarwa kan al'ummar kasar taawon kusan shekaru hudu.

Bangarorin biyu sun cimma matsaya kan batun bude filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Sana' da kuma gaggauta gudanar da sauran ayyuka na farfado da tattalin arzikin kasar, da kuma tilasta dakatar da bude wuta a garin Hudaidah, domin majalisar dinkin duniya ta samu damar shigo da kayyayaki.

3790998

 

captcha