IQNA

Tattaunawar Macron Da Putin Kan Batun Syria

23:09 - February 16, 2019
Lambar Labari: 3483379
Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin, sun tattauana ta wayar tarho kan halinda kasar Siriya ke ciki.

Kamfanin dillancin labaran iqna, alokacin tattaunarwa Mista Macron, ya bayyana damuwarsa kan tabarbarewar al'amura da kuma yadda hakan ke zaman babbar barazana a yankin da kuma duniya.

Sanarwar da fadar shugaban kasar Faransa ta fitar, ta kuma ce har kulun mahukuntan Paris na a shrye wajen hadin gwiwa da Rasha domin samar da mafita kan rikicin kasar ta Siriya.

A cewar sanarwar, hadin gwiwa na tsakanin kasashen na Rasha da Faransa, kan Siriyar, zai taimaka sosao wajen cimma gurin da aka sa a gaba.

Baya ga kare fararen hula, shugaba Macron ya ce abun da za'a a gaba shi ne yaki da kungiyar daesh da kuma gungun 'yan ta'adda wandanda kwamitin tsaro na MDD ya zayyana.

Wani batu mai wajabci da shugaba Macron ya tabo shi ne cewa a samar da hanya ta tattaunawar siyasa a shiga tsakanin MDD, domin samar da zaman lafiya da kuma maida 'yan gudun hijira kasarsu, da kuma tsara kudin tsarin mulki don kaiwa ga samar da sahihin zabe a kasar ta SIriya duk a cikin sanya ido na majalisar dinkin duniya.

 

3790664

 

 

 

captcha