IQNA

An Zargi Gwamnatin Najeriya Da Nuna Halin Ko In Kula Kan kisan ‘Yan Shia

23:54 - December 13, 2018
Lambar Labari: 3483212
Kungiyar ta kare hakkin bil'adama ta ce har yanzu gwamnatin kasar ta Najeriya ta kasa daukar matakan da su ka dace akan kisan da aka yi wa 'yan shi'ar a 2015

Kamfanin dillancin labaran iqna, Bayanin kungiyar kare hakkin bil'amar ta "Human Righr Watch' ya ce kisan na 'yan shi'a da jami'an tsaron kasar su ka yi, yana tattare da hatsarin jawo rashin yarda da tada kayar baya wanda zai kara dagula harkokin tsaro a kasar.

A watan Disamba na 2015 ne sojojin Najeriya su ka yi wa 'yan shi'ar kasar kisan kiyashi, tare kuma da kame shugabansu Sheikh Ibrahim Yakubu Al-zakzaky

Tare da cewa wata kotu a kasar ta yi kira da a saki shehun malamin, sai dai har yanzu ana ci gaba da tsare da shi tare da mai dankinsa Malama Zinat.

An zargi jami'an sojin njeriya da kashe magoya bayan harkar musulunci kusan dari uku da hamsin, tare da bizne su a cikin mayna kabruka na gama garia  Kaduna da ma wasu wurare da ba  asani ba.

Sai a nasu bangaren magoya bayan harkar musulunci sun ce adadin da sojoji suka kashe ya zarta wanda ake fada, inda suka fitar da sunayen mutane fiye da dubu daya wadanda babu babu labarinsu tun bayan harin da sojojin suka kai kansu a Zaria.

 

3771983

 

 

 

 

captcha