IQNA

Wani Kamfani Ya Samar Da Robobin Ruwa Miliyan 10 Ga Masu Ziyarar Arbaeen

23:42 - October 19, 2018
Lambar Labari: 3483057
Bangaren kasa da kasa, kamfanin samar da ruwan sha na kwalba na Naba a birnin Najaf na Iraki ya samar da robobin ruwa guda miliyan 10 domin masu ziyarar arbaeen.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin samar da ruwan sha na kwalba na Naba a birnin Najaf na Iraki ya samar da robobin ruwan sha guda miliyan 10 domin masu ziyarar arbaeen na Imam Hussain.

Bayanin ya ce kamfanin ya rika samar da rubobi dubu 300 ne a kowace rana tun daga makonnin da suka gabata, inda ya zuwa yanz ya tanadi robobi miliyan 10 na ruwan sha da zai raba su kyauta ga masu ziyarar Imam Hussain (AS).

3757057

 

 

 

captcha