IQNA

Kur'ani na Farko Mai dauke Da Hotuna Domin Kananan Yara A Birtaniya

23:52 - August 17, 2018
Lambar Labari: 3482899
Bangaren kasa da kasa, a karon farko an buga kur'ani mai dauke da hotuna domin amfanin kanan yara a kasar Birtaniya.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a karon farko an buga kur'ani mai dauke da hotuna domin amfanin kanan yara a kasar Birtaniya wanda shirin Sharif ta rubuta kuma ta buga, bayan samun izni daga majalisar fatawa ta musulmin kasar.

Ta ce wannan kur'ani ya kunshi juzui talatin, yana dauke da hutuna da suke ishara da wasu daga cikin ayoyi domin fahitar da yara abin da ayar ke Magana a kansa.

Haka nan kuma ta kara da cewa wannan kur'ani zai tasiri matuka wajen sanya shauki ga kananan yara domin mayar da hankali ga ayoyin da kuma abin da suka kunsa.

3739068

 

 

captcha