IQNA

A Bayar Da Kyautar Ban Girma Ta Birnin Paris Ga Dan kare Hakkin Bil Adama Na Bahrain

23:51 - June 18, 2018
Lambar Labari: 3482768
Bangaren kasa da kasa, a yau ma’aikatar magajin garin birnin Pais na kasar Faransa ta bayar da kyautar ban girma ga shugaban hukumar kare hakkin bil adama a kasar Bahrain Nabil Rajab.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, magajin garin birnin Paris ya bayar da kyautar ban girma ta birnin ga Nabil Rajab shugaban hukumar kare hakkin bil adama a kasar Bahrain.

Patrick Glogman mataimakin magajin garin birnin Paris da Shekh Maisam wani mai fafutukar kare hakkin bil adama su n suka gabatar da jawabi a wurin taron girmama Nabil Rajab a Paris.

An bayyana Nabil Rajab a matsayin wani warzo wanda ya bayar da rayuwarsa da lokacinsa domin kare hakkin bil adama da kuma kalubalantar zaluncin masarautar kama karya ta kasar Bahrain.

Sakamakon irin wadannan matakai da yake dauka na nuna rashin jin tsoron azzaluman sarakunan larabawa musamman na masarautar kama karya ta Bahrain, wannan masarauta ta kame shi tare da yanke masa hukuncin daurin shekaru biyar a gidan kaso.

Wannan mataki yana ci gaba da fuskantar kakkausar suka da Allawadai daga kasashen duniya masu sauran lamiri, kamar yadda kuma kungiyoyin kare hakkin bil adama suke ci gaba da yin fafutuka domin ganin an sake shi.

3723433

 

 

 

captcha