Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a lokacin da take yin magana a jiya shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Mrkel ta bayyana cewa, kafin daukar duk wani matakin soji a kan Syria, dole ne a yi bincike a dukkanin bangarori.
Ta kara da cewa, a iyakacin sanina dai har yanzu ba a yanke mataki na karshe ba kan batun kaddamar da hari kan kasar Syria.
Markel ta jaddada cewa, wajibi ne kasashen turai su tababtar da cewa bakinsu ya zo daya kafin daukar duk wani matakin soji a kan Syria, kuma muna jiran sauran sauran kasashen turai da suke da wannan aniya da su shawara da mu.
A ranar Laraba da ta gabata ce dai shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar kai hari kan kasar Syria, bisa zargin cewa gwamnatin kasar ta yi amfani da makaman nukiliya kan ‘yan ta’adda, amma Rasha ta mayar da martini da cewa za ta kakkabo duk wani makami da Amurka za ta harba a kan Syria.