Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin muslimlink.ca cewa, a ranar 25 ga watan Maris mai kamwa ne za a gudanar da wannans hiri tare da halartar musulmi.
Wannans hiri dai zai kunshi bayanai da kuma baje koli na kayayyakin musulunci da suka hada da littafai, da kuma kayan fasaha, gami da wasu daga cikin alluna masu dauke da bayani kan a cikin hoto.
Baya ga haka kuma za a nuna wasu daga nauin kayan abinci na Halal da musulmi suke yin amfani da su musamman a lokacin azumin watan Ramadan mai alfarma.
Alkur'ani mai tsarki dai yana a matsayin littafin dukkanin musulmi baki daya, yayin da kuma sunnar manzon Allah take a matsayin mai fassara shi, kamar yadda kuma za a nuna wasu daga cikin kayan ashura a wurin bajen kolin.