IQNA

Gasar Kur'ani Mai Tsarki Ta Hanyar Facebook

22:45 - February 17, 2018
Lambar Labari: 3482403
Bangaren kasa da kasa, ana gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki ta hanyar facebook mai taken (The Voice Quran) wadda matasan kasar Masar suke gudanarwa.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin jaridar yaum sabi cewa, wannan gasa wasu gungun matasan kasar Masar ne suka kirkiro ta, da nufin yada lamarin kur'ani mai tsarki ta hanyar yanar gizo a tsakanin takwarorinsu matasa.

Wannan dais hi ne karon farko da aka kirkiro gasar kur'ani mai tsarki kuma ake gudanar da ita ta hanyar yanar gizo.

Gasar dai ta hada maza da mata, amma dukkaninsu kowanne an kebe musu bangaren da za su gudanar da tasu gasar, kamar yadda kuma an kayyade shekarun masu gudanar da gasar, kan cewa dole ne su zama matasa kasa da shekaru ashirin.

Masu gudanar da gasar dai suna aikewa ne da faifan bidiyo da suka dauka suna karatun kur'ani na tsawon mintuna akalla uku, tare da cikakken bayanin adireshinsu.

Za a kamala wannan gasar ne a cikin makonni biyu masu zuwa kuma za a bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka fi nuna kwazo.

3692137

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha