IQNA

Kasashen 56 Ne Za Su Halarci Taron OIC

20:58 - February 15, 2018
Lambar Labari: 3482398
Bangaren kasa da kasa, Kungiyar kasashen musulmi ta OIC za ta gudanar da wani zaman domin yin dubi a kan matsalar rashin ayyukan yi a kasashen musulmi, da kuma samo hanyoyin tunkarar matsalar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Kamfanin dillancin labaran INA ya bayar da rahoton cewa, zaman wanda zai gudana a birnin Jidda na kasar saudiyya a mako mai zuwa, zai samu halartar ministocin ayyuka daga kasashe 56, gami da wakilai daga kasashe masu sanya idoa  kungiyar da kuma kungiyoyi na kasa da kasa.

Babbar ajandar taron dai ita ce, yin dubi kan matsalolin da ake fuskanta a kasashen musulmi ta fuskar harkokin kasuwanci da kuma rashin ayyukan yi a tsakanin matasa musamman, da kuma yadda za a fuskanci matsalar domin warware ta.

Daga cikin abubuwan da za a tattauna kan hakan akwai batun bunkasa taimakekeniya tsakanin kasashen, da kuma musayar ma'aikata bisa masaniya da kuma gogewa da suke da ita a wasu bangarori na aiki, da kuam wasu batutuwan da suka shafi zuba hannayen jari a bangaren samar da ayyuka a cikin kasashen musulmi.

3691377 

 

captcha