IQNA

An Raba Kwafin Kurnai Domin Amfanin makafi A Kasar Morocco

22:42 - February 13, 2018
Lambar Labari: 3482392
Bangaren kasa da kasa, an raba kwafin kur'anai da aka yi amfani da fasaha ta musamman a kansu domin amfanin makafi.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na hespress.com cewa, wadannan kur'anai an raba su ne tare da taimakon cibiyoyin Mawadda ta UAE da kuma Tasnim ta Malaasia.

Ana yin amfani da wani alkami na musamman ne wajen karatun, inda makafi da marassa gani za su iya karanta kur'ani ta hanyar yin amfani da wanna alkalami na musamman.

Mustafa Khalfi ministan sarawa na kasar Morocco ya fadi a wajen raba wanann kur'ani cewa, hakika wannan zai taimaka ma masu fama da larurar gani wajen karatun kur'ani mai tsarki.

Ya kara da cewa wannan wata dam ace da aka samu wadda fasahar zamani ta zo da ita, saboda haka dole ne a yi amfani da ita domin amfanin masu larurar gani, domin kuwa su ma suna da hakki kamar sauran al'umma, duk wata dama da aka samu dole a yi amfani da domin taimakonsu.

Ibrahim Yaarabi wakilin cibiyar Mawadda ta UAE ya fadi a wurin cewa, sun yi kokari sun samar da irin wannan kwafin kur'ani guda dubu biyar, kuma za su ci gaba da yin hakan a nan gaba.

3691260

 

 

 

captcha