IQNA

Daruruwan Mutane Sun Rasa Rayukansu A Harin Ta’addanci A Masar

23:42 - November 24, 2017
Lambar Labari: 3482133
Bangaren kasa da kasa, Akalla mutane 235 ne aka tabbatar da sun rasa rayukansu a yau, sakamakon wani hari da 'yan ta'adda masu dauke da akidar wahabiyyah takfiriyyah dake da'awar jihadi tare da kafurta musulmi suka kaaddamar a masallacin Raudha, da ke birnin Al arish a gundumar Sinai, a lokacin da musulmi suke gudanar da ibadar sallar Juma'a.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Wasu gungun 'yan ta'adda sun farma wani Masallacin Juma'a a lardin Sina ta Arewa da ke kasar Masar, inda suka kashe mutane fiye da 230 tare da jikkata wasu fiye da 100 na daban.

Majiyar tsaron Masar ta sanar da cewa: Wasu gungun 'yan ta'adda sun farma wani Masallacin Juma'a a garin Arisha da ke lardin Sina ta Arewa na kasar Masar a lokacin sallar Juma'a a yau, inda suka bude wuta tare da tayar da bama-bamai a tsakanin masallata lamarin da ya janyo mutuwar mutane akalla 235 tare da jikkata wasu giye da 100 na daban.

Har yanzu dai babu wata kungiya ko jama'a da suka dauki alhakin kai wannan mummunan harin ta'addanci amma dai ana nuna yatsar zargi kan kungiyar Ansaru-Baiti Maqdis da ta sanar da hadewarta da kungiyar ta'addanci ta Da'ish a shekara ta 2014, kuma wannan kungiyar ce ta yi kaurin suna a fagen kai hare-haren wuce gona da iri a lardin Sina ta Arewa.

Kasashen duniya da kungiyoyi suna c gaba da yin Allah wadai da hakan, inda a nata bangaren Iran ta yi Allah wadai da kakkausar murya, dangane da wannan harin ta'addancin da Takfiriyawa suka kai kan masallacin Raudha a birnin Al-arish na Masar a yau a lokacin sallar Juma'a, lamarin da ya yi sanadiyyar yin shahadar masallata 235.

Bayanin na gwamnatin Iran ya ce; wannan harin ya kara tabbatar da cewa addinin muslunci daban akidar ta'addanci da sunan jihadi daban, domin kuwa hatta wuraren ibada na al'ummar musulmi da ake bauta ma Allah da ambatonsa, ba su tsira daga sharrin wadannan mutane masu dauke da wannan mummunar akida ba.

3666463


captcha