IQNA

Limamin Juma’a A Tehran:

Gudunmawar Jagora, Ayatollah Sistani, Janar Sulaimani wajen Karya Lagon Daesh

23:40 - November 24, 2017
Lambar Labari: 3482132
Bangaren kasa da kasa, Hojatol Isam Siddiqi wanda ya jagoraci sallar Juma’a a Teran ya bayyana wajacin zama cikin fadaka domin tunkarar makircin Amurka a kan al’ummar yankin gabas ta tsakiya, musamman a halin yanzu bayan murkuse ‘yan ta’addan da ta kafa a yankin tare da taimakon sarakunan larabawa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Limamin da ya jagoranci sallar Juma'a a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran ya bayyana cewa: Kawo karshen kungiyar ta'addanci ta Da'ish gagarumar nasara ce a kan makircin gwamnatin kasar Amurka da 'yar korenta haramtacciyar kasar Isra'ila.

A hudubar sallar Juma'arsa ta yau a babban Masallacin birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran: Hujjatul-Islam Kazim Sadiqi ya bayyana cewa: Gwamnatin Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila sun kafa kungiyar ta'addanci ta Da'ish ce da nufin kunna wutan rikici da tashe-tashen hankula a yankin gabas ta tsakiya amma sai mummunar aniyarsu ta kasa cimma nasara.

Hujjatul-Islam Sidiq ya kara da cewa: Kungiyar ta'addanci ta Da'ish ta tafka munanan ayyukan cin zarafin bil-Adama musamman aiwatar da dangogin kashe-kashen gilla mafi muni a tsawon tarihi da suka hada da fille kan mutane, kona su a raye, nutsar da mutane a cikin ruwa har su mutu, turo su daga kan dogayen benaye, tada bama-bamai a cikin Masallatai da wajajen taron jama'a da sauransu.

Har ila yau Hujjatul-Islam Kazim Sidiqi ya fayyace cewa: Makiya suna kokarin ganin sun bata sunan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a idon duniya amma kullum kasar sai samun ci gaba take yi a bangarori da dama.

Amurka da tare da ‘yan korenta daga cikin larabawa na yanin gabas ta tsakiya, gai da haratacciyar kasar yahudawan sahyuniya, suna da shirin ganin sun kawo ma Iran cikas a dukkanin lamurranta, sakamakon yada ta zama karfen kafa wajen cimma munana bakaken manufofins a kan al’ummar musulmi.

3666448


captcha