IQNA

Cibiyar Azhar Ta Yi Allah wadai Da Harin Ta’addanci A Najeriya

22:58 - November 23, 2017
Lambar Labari: 3482130
Bangaren kasa da kasa, cibiyar Azhar da ke kasar Masar ta fitar da bayanin yin tir da Allah wadai da harin ta’addancin da aka kai a Mubi da ke jahar Adamawa.

Kamfanin dillancin abaran iqna ya habarta cewa, cibiyar Azhar da ke kasar Masar ta fitar da bayanin yin tir da Allah wadai da harin ta’addancin da aka kai a Mubi da ke jahar Adamawa wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da hamsin.

Azhar a cikin bayanin ta bayyana cewa, wannan abin da ya faru a Najeriya yana daga cikin sakamako na yaduwar akidar ta’addanci da sunan adini, wanda hakan ya yi hannun riga da hakikanin koyarwar addinin muslunci.

Haka nan kuma bayanin ya kira a kan wajabcin yaki da ta’addanci tun daga asasi, domin kuwa da karfi ba za a iya kawar da ta’addanci ba domin kuwa akida ce wadda wahabiyanci ne tushenta, amma ta hanyar yaki da wannan akida a ilmance da kuma hanyoyi na fadakarwa, za a samu nasara wajen rage kaifin lamarin.

Ita ma a nata bangaren kungiyar kasashen musulmi ta yi tir da Allah wadai da wannan aiki na ta’addanci, inda aka kai hari kan masalata da suke sallar asubahi a garin Mubi na jahar Adamawa, inda mutae fiye da 5 suka sara rayukansu, wasu kuma suka jikkata.

3665851


captcha