Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Jagoran jiyun juya halin musulinci ya tabbatar da cewa: jamhuriyar muslunci ta Iran ta tsaya tsayin daka kuma za ta ci gaba da tsayawa wajen tunkarar makircin girman kai da harmtacciyar kasar Iran na samar da yaki tare da sanya sabani a tsakanin al'ummar musulmi, da yardar Ubangiji kuma za ta ci nasara a wannan yaki.
A yayin ganarwa da mahalarta taron masoya iyalan gidan Anabta
tsarkaka da kuma batun masu akidar kafirta mutane a safiyar yau Alhamis,
Jagoran juyin juya halin Muslunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce
duk da cewa an kusa kawo karshen ta'addancin kungiyar IS a kasashen
Iraki da Siriya, amma kada mu gafala da makircin makiya saboda Amurka da
HKI gami da kawayensu ba za su taba daina kiyayya da musulinci ba, kuma
mai yiyuwa su sake kula wani makirci wajen samar da wata kungiya irin
ta IS a wani yankin. Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce a yau duniyar musulinci na
bayan gaskiya guda ne fada da kafirci gami da girman kai, tsarin
musulinci a nan Iran kuma na bayan tabbatar da shari'ar musulinci ne
wanda hakan ita ce hanya daya tilo na cin nasara a kan makiyan
musulinci a duniya. A yayin da yake ishara kan kimanin kusan shekaru 40 da makiya suka
kwashe suna kula makirci a kan tsarin musulinci ta hanyar sanya
takunkumi da matsin lamba, jagora ya ce duk da matsin lambar makiya, a
hakikanin gaskiya ina bayyana muku cewa jumhoriyar musulinci ta Iran a
duk inda ake kalubalantar kafirci da girman kai, idan akwai bukatar
taimako, za mu taimaka, kuma a game da wannan batu ba za mu saurari
wani mutum ba. Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya
ce maganar Palastinu ita ce mas'alar farko ga duniyar musulinci ,
mabudin cin nasara a kan makiyan musulinci shi ne maganar Palastinu
saboda manufar makiya na samar da rashin tsaro da kuma sanya sabani a
kasashen musulinci shi ne mantar da al'umma batun Palastinu, tare da
tabbatar da cewa ranar da Palastinu za ta koma ga al'ummar Palastinu,
ita ce ranar da gadan bayan makiya zai karye kuma ita ce babbar rana ta
cin nasarar al'ummar musulmi, domin tabbatuwar hakan za mu iya namu
kokari.