IQNA

Sayyid Hassan Nasrullah:

An Murkushe Daular Daesh A Syria Da Iraki / Jinjina Ga Janar Qasim Sulaimani

23:46 - November 20, 2017
Lambar Labari: 3482120
Bangaren kasa da kasa, babban sakataren kungiyar Hizbullah ya bayyana murkushe 'yan ta'addan wahabiya na Daesh a Bukamal a matsayin kawo arshen daularsu yanzu sai dai 'ya'yan kungiyar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Shugaban kungiyar hizbullah sayyid Hasan Nasrullah ya bayyana cewa a halin yanzu gwamnatin kungiyar ta'addanci IS ta kawo karshe a kasashen Siriya da Iraki kuma nan ba da jimawa ba za a gudanar da bikin kawo karshen Da'esh

Cikin wani jawabi da ya gabatar a marecen wannan litinin, shugaban kungiyar hizbullah ta kasar labnon ya gabatar da ta'aziyarsa ga al'ummar Iran game da girgizar kasar da ta auku makun da ya gabata a jumhoriyar musulinci ta Iran, sannan kuma ya bayyana irin nasarorin da kungiyoyin gwagwarmaya suka samu a kasashen Iraki da siriya, inda ya ce a halin da ake ciki an kawo karshen daular ta'addanci ta da'esh kuma nan ba da jimawa ba za a gudanar da bikin kawo karshen Da'esh,

Sayid Nasrullah ya ce Amurka ta yi iya kokarinta wajen tseratar da mayakan da'esh daga yankin Bukmal, a yayin da dakarun gwagwarmaya suka fatattake su.

Yayin da yake mayar da martani game da sanarwa taron ministocin harkokin kasashen wajen larabawa da ya gudana jiya lahadi a birnin alkahirar Masar, sayid Hasan Nasrullah ya ce wannan ba wani sabon abu ne kiran kungiyar da sunan kungiyar ta'addanci domin mahalarta taron suna karnata abinda aka rubuta musu ne daga magabatan birnin Riyad kuma wannan siyasar Amurka ce na sanya duk wata kungiyar gwagwarmaya ko wani mutum da yake gwagwarmaya da manufofinsu a yankin gabas ta tsakiya za a sanya kungiyar ko mutuman a cikin jerin 'yan ta'adda.

Har ila yau sayid Hasan Nasrullah ya musanta zargin da taron kungiyar kasashen larabawan suka yiwa kungiyar Hizbullah na cewa kungiyar na tura manyan makamai masu hadari da kuma makamai masu lizzami zuwa kasashen Larabawa, sannan sun ce mayakan kungiyar Hizbullah ne suka harba makamai mai lizzami daga kasar yemen zuwa filin jrgin birnin Riyad na kasar Saudiya, inda ya ce wannan zarki ne kawai da ba shi da wani tushe.

Sayid Hasan Nasrullah ya ce ba su taba tura wani makami ko harshashi guda zuwa wata kasar larabawa ba, face zuwa Palastinu kuma wannan abin alfahari ne a gare su.

3665279


captcha