IQNA

Makarancin Kur'ani Dan Masar A Taron Karatun Kur'ani A Basarah

19:52 - November 18, 2017
Lambar Labari: 3482112
Bangaren kasa da kasa, kungiyar makarantar kur'ani ta Basara a Iraki ta bayyana cewa daya daga cikin makarantan kur'ani na Masar ya halarci taron kur'ani a birnin.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na QAF cewa, a jiya kungiyar makarantar kur'ani ta Basara a Iraki ta bayyana cewa daya daga cikin makarantan kur'ani na Masar ya halarci taron kur'ani a birnin a bababn masalalin Milak, karkashin kulawar wakilin Ayatollah Sistani.

Bayanin ya ci gaba da cewa makarancin kur'ani Muhammad Nazzar da kuma wani makarancin Muhammad Sattar, sun gabatar da karatu a wurin.

Taron dai an shirya shi ne domin tunawa da zagayowar lokacin wafatin manzon Allah (SAW) wanda aka saba gudanarwa akowace shekara a sasa daban-daban na kasar Iraki da ma wasu kasashen duniya.

Daga karshen taron na jiya Nasir Harak dan kasar Masar kuma makarancin kur'ani ya gabtar da karatu da sautinsa mai kyau, inda jama'a suka saurara.

Wannan makaranci dai yana daga cikin makaranta na Masar ad suka kammala karatua jami'ar Azhar da ke birnin kahira a bangaren ilmomin kur'ani.

3664559


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha