IQNA

Sayyid Ahmad Khatami:

Lamarin Arbaeen Lamari Ne Na Addini / Saudiyya Tana shirin Haifar Da Babbar Fitina A Yankin

0:00 - November 11, 2017
Lambar Labari: 3482087
Bangaren siyasa, wanda ya jagoranci sallar Juma’a a yau a Tehran ya bayyana fitowar miliyoyin jama’a wajen raya tarukan arbaeen da cewa babban lamari ne a cikin addini, yayin da masarautar ya’yan saud ke hankoron haifa da fitina a yankin gabas ta tsakiya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Limamin da ya jagoranci sallar Juma'a a birnin Tehran ya bayyana cewa: Murabus da fira ministan Lebanon Sa'ad Hariri ya yi daga kan mukaminsa a kasar Saudiyya lamari ne da ke fayyace irin tsoma bakin da mahukuntan Saudiyya suke yi a harkokin cikin gidan kasar ta Lebanon.

A hudubar sallar jum'arsa ta yau a babban Masallacin birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran: Hojjatol Islam Sayyid Ahmad Khatami ya fayyace cewa: Mahukuntan Saudiyya suna kokarin kunna wutan rikici da mummunar dambaruwar siyasa a kasar Lebanon, kamar yadda suke da hannu dumu-dumu a tashe-tashen hankulan da suke faruwa a kasashen Iraki, Siriya, Yamen da Lebanon.

Hojjatol Islam ya kara da cewa: A fili yake mahukuntan Saudiyya sun tilastawa Sa'ad Hariri yin murabus daga kan mukaminsa na fira ministan Lebanon ta hanyar karanta takardar da suka gabatar masa a matsayin jawabinsa lamarin da yake matsayin tsoma baki karara a harkokin cikin gidan kasar ta Lebanon.

Har ila yau Hojjatol Islam Khatami ya fayyace kame-kamen 'ya'yan gidan sarautar Saudiyya da mahukuntan kasar ke yi a matsayin wani sabon salon makirci. Kamar yadda furuci da barazanar da yarima mai jiran gadon Saudiyya Muhammad bin Salman ke yi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran zasu fuskanci maida martani mai gauni daga al'ummar Iran.

Daga karshe ya ja kunnen masu rike da madafun iko a Saudiyya tare da manyan kawayensu wato yahudawan Isra’ila, da su shiga taitayinsu, domin kuwa tunkarar Iran da sunan yakia halin yanzu ba lamari ne mai sauki ba.

3661769


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha