Tattaunawa Tsakanin Shi'a Da Ahlul Suna Tafi Muhimmanci Da Ta Tsakanin Musulmi Da Kirista
Bangaren kasa da kasa: musulmin na kokarin bude wani fage da fada shit a fuskar tattaunawa da fahimtar juna a tsakaninsu da kiristoci alhali kuwa abin da yafi dacewa shi ne samar da wani fili da fage na tattaunawa tsakanin musulmi mabiya mazhabar shi'a da kuma yan uwansu musulmi mabiya sunna kuma wannan musamman idan aka yi la'akari akwai abubuwa da dama da suka kasa fahimtar juna a kansu alhali abubuwa masu kima da daraja sun hada su guri guda.
Za A Gyara Masallacin Farko A Musulunci Da Ke Yankin Quba A Kusa Da Madina
Bangaren kasa da kasa, ana shirin fara gyaran masallacin Quba wanda shi ne masallacin farko a cikin addinin muslunci da ke kan hanyar isa birnin madina daga Makka kamar dai yadda maa'ikatar kula da harkokin addini ta kasar Saudiyya ta sanar.