IQNA

Kira Domin Janye Haramcin Gudanar Da Tarukn Ashura A Kashmir

23:46 - September 06, 2019
Lambar Labari: 3484022
Bangaren kasa da kasa, wani mai fafutuka a yankin Kashmir ya kirayi mahukuntan India da su janye haramcin gudanar da tarukan Ashura.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Sayyid Karrar Hashemi wani mai fafutuka a yankin Kashmir ya kirayi mahukuntan India da su janye haramcin gudanar da tarukan Ashura da suka sanya a yankin. 

Ya ce daukar wannan mataki a kan musulmin yankin musamman mabiya mazhabar shi’a wadanda suke gudanar da tarukansu daruruwan shekaru a  wannan yankin, hakan na a matsayin take hakkokinsu.

Haka nan kuma ya aike da wannan kira nasa da ya yia  cikin wani rubutaccen bayani zuwa mahukuntan kasar ta India, da suka hada da frayi minister da kuma wasu manyan mutane masu tasiria  kasar.

Mabiya mazhabar shi’a suna gudanar da tarukan ashura a yankin Kashmir da sauran yankuna an India sawon daruruwan shekaru, inda wanan shi ne karo na farko da gwamnatin India ta hana su yin hakan a Kashmir.

Wannan matai dai na zuwa sakamakon zaman rashin tabbas da ake a yi a yankin an Kashmir, biyo bayan soke kwarya-kwaryan cin gishin kan da yankin na Kashmir na India yake da shi.

3840376

 

 

captcha