IQNA

Gwamnatin Nicaragua Za Ta Bude Ofishinta A Palestine

23:38 - August 08, 2019
Lambar Labari: 3483925
Bangaren kasa da kasa, Gwamnatin kasar Nicaragua na shirin bude ofishin jakadanci a birnin Ramallah fadar mulkin gwamnatin Falastinawa.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na Watan ya bayar da rahoton cewa, jakadan falastinu a majalisar dinkin duniya Rayadul Maliki ya sanar da cewa, gwamnatin kasar Nicaragua na da niyyar bude ofishin jakadancinta a Palestine.

Ya ce jami’an diflomasiyyar kasar ta Nicaragua sun sanar da shi cewa, suna cikin shirin bude ofishin jakadanci a birnin Ramallah nan ba da jimawa ba, kuma za su ci gaba da tuntubar juna domin kammala dukkanin shirin da ya kamata kan hakan.

Wannan mataki na Nicaragua na zuwa a matsayin wani martani ga matakin da Amurka ta dauka na mayar da ofishin jakadancinta zuwa birnin quds, da nufin muzgunawa falastinawa da kuma kwace hakkinsu na mallakar brnin.

 

3833497

 

 

 

captcha