IQNA

Azhar Ta Yi Allawadai Da Hare-Haren Da Aka kai Amurka

23:42 - August 05, 2019
Lambar Labari: 3483916
Bangaren kasa da kasa, cibiyar Azhar da ke kasar Masar ta yi tir da hare-haren da aka kai a jihohin Texas da Ohiyo na kasar Amurka.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cwa, a cikin bayanin da cibiyar ta Azahr ta fitar a jiya, ta bayyana harin da aka kai a jihohi biyu na Amurka da cewa abin Allawadai ne.

Wani dan bindiga ne ya kai hari a ranar Asabar a jihar Texas ta kasar Amurka, ya harbe mutane akalla ashirin har lahira, tare da jikkata wasu da dama.

A nasu bangaren Jami’an tsaro sun bayyana cewa, mutumin ya fara harbe-harbe da bindiga ne tun daga wani wurin ajiye ababen hawa, kafin daga bisani ya shiga cikin rukunun shaguna Cielo Vista Mall da ke garin El Paso da ke cikin jihar Texas a kusa da iyaka da kasar Mexico.

Bayanin jami’an tsaron ya ce an samu nasarar cafke mutumin, ba tare da sun yi wani Karin bayani kan dalilansa na yin hakan ba.

Harin ya fuskanci tir da Allawadai daga mahukuntan kasar ta Amurka, kamar yadda jama’a a yankin suka bayyana harin da cewa ya yi muni matuka.

Bayan wanann hari an kai wani makamancinsa a garin Daiton na jihar ohio, inda a can ma wani dan bindiga ya kashe fararen hula tara har lahira.

Kasar Amurka ce kasar da tafi kowace kasa fuskantar irin wadannan hare-hare da mutane suke kaiwa kan jama’a, ko dai saboda dalilai na kuncin rayuwa, ko kuma saboda shaye-shaye na kwayoyi masu bugar da hankali.

 

3832572

 

 

captcha